Zan İya yin Sulhu da ‘Yanbindiga İdan Sun Mika Wuya- Gwamnan Zamfara

Share

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan ya ce zai iya yin sulhu da ƴanbindiga idan har sun ajiye makamansu.

Gwamnan ya ce amma sai ƴanbindigar sun daina kashe mutane kuma sun ajiye makamansu sannan za a iya yin sulhu da su.

A hirarsa da BBC, Gwamna Dauda ya bayyana cewa ba wai ba za a iya yin sulhu da ƴanbindigar bane, “Amma koda za ka yi sulhu kayi shi a kan gaskiya, ai.

“Akwai da yawa wadanda aka cutar da su, wasu an kashe iyayensu wasu matansu, saboda haka sai a duba me za a yi masu saboda sun rasa dukiyarsu, bawai kullum a riƙa fitfita ƴanbindiga ba.

Gwamna Dauda ya bayyana cewa suna samun nasara a yaƙin da suke da ƴanbindiga, “An kashe ƴan ta’adda fiye da 50 a ranar Juma’a a garin Tingar Fulani, wajen Zurmi da Shinkafi.”

“Akwai manya-manyan kachalloli da yanzu haka sun tafi lahira, wadanda suke tare da Bello Turji, akwai Sani Mainasara da Sani Black da Kachallah Auta, Audu Gajere da Kabiru Jangero, Dangajere da makamantansu, duk an hallakasu,” a cewar Dauda Lawal.

Gwamnan ya ce wannan nasara da ake samu za a ci gaba da samunta har sai na kai ƙarshen lamarin, Kodai su aje makamansu ko kuma mu ba zamu bar su ba.”

Abaya dai, Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya sha nanata cewa har ba zai yi sulhu da ƴan fashin daji ba.

Yayin zantawarsa da BBC gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matsaya ne ganin cewa a bayan an sha yin sulhu da ‘yan bindigar, amma ba sa mutunta alƙawurran da aka yi da su a baya.

”An yi sulhun nan a baya ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma an kasa cimma ake abin da ake so”, in ji gwamnan.

Duk da dai ikirarin hukumomi na yaƙar ƴanbindiga a yankin arewa maso yammaci, kusan a kullum sai an kai hari musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.

Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin johohin da matsalar tsaro ta fi kamari a faɗin Najeriya, inda barayin daji ke afkawa garuruwa da kauyuka da kashe mutane da satar wasu domin neman kuɗin fansa, ga kuma sacewa ko kwace amfanin gonar da manoma suka shuka.

#BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *