Manchester United ta shirya gabatar da tayin fam miliyan 33.3 kan ɗan wasan Barcelona mai shekara 21 daga Sifaniya, Alejandro Balde a wannan kaka. (El Nacional – in Spanish)
Newcastle na shirin taya ɗan waan PSV Eindhove mai shekara 21, Johan Bakayoko kan fam miliyan 33.3. (Tuttosport – in Italian)
Newcastle na kuma son doke Barcelona da Real Madrid kan ɗan wasa Antonio Cordero, mai shekara 18 da kwantiraginsa ya kare da Malaga. (Mail)
BBC Hausa Ta Ruwaito Cewar Manchester United da Chelsea na farautar ɗan wasan Ipswich mai shekara 22, Liam Delap. (Football Insider)
Chelsea ta kwaɗaitu da ɗan wasan Copenhagen mai shekara 19 daga Sweden, Roony Bardghji. (TBR Football)
Fiorentina na duba yiwuwar gabatar da sabon kwantiragi kan, Moise Kean wanda zai kara masa daraja, yayinda ƙungiyoyin Firimiya irinsu Tottenham da Arsenal ke nuna zawarcinsu kan matashin na Italiya mai shekara 24. (Corriere dello Sport via Calciomercato – in Italian)
Chelsea na bibbiyar ɗan wasan Sporting mai shekara 19, Dario Essugo, da ke zaman aro a Las Palmas. (Fabrizio Romano)
Ɗan wasan Bournemouth mai shekara 19 daga Netherlands amma haihuwar Sifaniya, Dean Huijsen na son zuwa Chelsea. (Teamtalk)
An faɗawa kocin Real Madrid Carlo Ancelotti cewa yana da zaɓin yanke hukunci idan zai je Brazil domin horasa da tawagarsa zuwa watan Mayu. (OK Dario – in Spanish, external)
Arsenal na son saye mai tsaron raga a Espanyol mai shekara 23, Joan Garcia a wannan kaka. (Football Insider)
Manchester United na son daraktan wasanni a Athletic Bilbao, Mikel Gonzalez ya maye gurbin Dan Ashworth a Old Trafford. (El Chiringuito via Football Espana).