Hukumar Alhazai ta kasa ta bayyana nasarar biyan tantunan Alhazai dubu 26,287 a Masha’ir tare da kama wasu dubu 26,000 da zata biya zuwa Juma’a 13 ga watan Fabreru da zarar kudaden Alhazan sun shiga asusunta. Ana hasashen ‘yan Najeriya dubu 52 za su gudanar da aikin hajjin bana.Hanzarin kama tantunan Alhaza a Masha’ir da Shugaban hukumar Alhazai ta kasa , Parpesa Abdullahi Sale Usman ya jagoranta, ya nuna aiki da wa’adin da Saudiyya ta bayar na kitse duk wata yarjejeniyar da ta shafi aikin hajjin na bana a ranar 14 ga watan Fabrerun nan.
A ranar 17 ga watan Janeru wannan shekarar ne Parpesa Abdullahi Sale ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shirye shiryen aikin hajjin na bana bayan tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki musamman shugabanin kungiyar sakatarorin alhazai na jahohi da mambobin hukumar Nahcon dama wakilin fadar Shugaban kasa. Wadanda ke cikin tawagar da suka tantance kamfanonin da za su yi wa Mahajjatan Najeriya hidima.
Domin tabbatar da alhazan Najeriya sun samu biyan bukata yayin aikin na bana ne Parpesa Abdullahi ya nemi izini daga mataimakin Shugaban kasa, Sanata Kasim Shettima ya je Kasar Saudiyya domin karkare yarjejeniyar da ke da matukar muhimmanci wajen bada bizar Alhazai wadda za a fara ranar 19 ga wannan watan na Fabreru.
Parpesa Abdullhi ya bayyana godiyarsa ga Mataimakin Shugaban kasa bisa goyon bayan da yake ba su da rashin tsoma bakinsa a harkokin hukumar wanda ya ba su damar daukar matakan da suke ganin za su saukaka aikin hajjin bana.
Parpesa Abdullahi ya yi kira ga maniyyata da su rika bibiyar shafukan sadarwa na hukumar Nahcon domin samun karin bayanai kan hajjin na bana. Su kuma kwantar da hankulansu da cewa ana nan ana matukar kokari na ganin sun gudanar da aikin hajjin cikin jin dadi da walwala.