Gwamnatin Jihar Katsina Ta Raba Awaki ga Mata

Share

Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bai wa mata 3,610 da ke gundumomi 361 tallafin awaki wanda ya laƙume kuɗi naira biliyan 5.4 a matsayin tallafi.

Gwamnan Jihar Dikko Radda ya faɗi hakan ne a yayin da ya ke rabon awakin karkashin shirin kiwon awaki da aka ƙaddamar a garin Dan-Nakolo da ke karamar hukumar Daura.

Ya ce shirin wani babban mataki ne na cimma burinsu na ganin jihar Katsina ta zama kan gaba wajen yin kiwo a arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

Gwamnan jihar ya kuma ce karkashin shirin za a horar da matan kan matakan kiwo da suka dace da su, kamar abincin da ya kamata su ci, kula da lafiyarsu, da ma dabarun noma.

”Akalla awaki 40,000 aka ware domin rabawa waɗanda za su ci gajiyar shirin daga matakan gunduma inda duk gunduma aka zabo mata goma da babban manomi ɗaya, kuma duk mace daya za a ba ta awaki huɗu babban manomin kuwa awaki 50.”

Ya kuma ce a wannan shekarar za a kafa gonar kiwon awaki a karamar hukumar Rimi domin inganta kiwo, samun madara da kuma taki, kuma zai kasance cibiyar horaswa.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *